Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a wanna mako Ayatollah Rafsanjani ne zai jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran, amma kafin gudanar da hudubar juma'a bayan kamala karatun kur'ani mai tsarki za a gabatar da wasu jawabai da suka shafi ayyukan da kwamitin kula da ayyukan agaji na Imam Khomeni (RA) ke gabatarwa, inda mai kula da wannan kwamiti zai bayyana wasu daga cikin nasarorin da wannan kwamiti ya samu wajen gudanar da ayyukansa tun bayan kafa shi.
Bayan nan kuma wanda zai jagorancin sallar juma'ar Ayatollah Hashemi Rafsanjani zai gabatar da huduba.
369429