Bangaren adabi: A karon farko za a kafa wani kwalejin horar da masu tarjamar kur'ani a kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; bisa la'akari da cewa littafin kur'ani shi ne madogara mafi muhimmanci a wajen gudanar da bincike a cikin addinin musulunci, cibiyar da ke kula lamurran tarjamar kur'ani tare da hadin gwiwa tsakaninta da cibiyar kula da al'adu da sauran ayyukan addini, za su kafa wata kwalejin tarjamar kur'ani, wadda za ta kula da horar da masu tarjama.
Cibiyar tarjama da aka kafa a shekara ta 1373 hijira shamsiyya, kimanin shekaru 14 da suka gabata, ita ce za ta shiga kan gaba wajen gudanar da shirin na kafa kwalejin horar da masu tarjamar kur'ani mai tsarki, wanda kuma wannan shi ne karo na farko da za a gudanar da irin wannan aiki.
369375