IQNA

Ba A Tilasta Wa Iraniyawa Karbar Addinin Musulunci A Lokacin Manzon Allah (SAW) Ba

Bangaren fikra da ilimi: Tarihi ya tabbatar da cewa akwai alamu da dama da suke nuni da cewa, bisa la'akari da al'adun Iraniyawa a zamanin da, babu gaskiya cikin batun tilasta musu karbar addinin addinin musulunci a zamanin ma'aiki (SAW)
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; wani malamin jami'a mai suna (Muhammd Bagistani) wanda malamin tarihi ne a jami'ar mashhad ya bayyana cewa; Iraniyawa mutane masu tsoffin al'adu, kuma sukan karbi abin day a zo musu don radin kansu, kuma mutane ne da ba a tilasta su bin abin da ba su natsu da shi ba, bisa dogaro da wadannan dalilai da tarihi ya tabbatar da su za a iya cewa, batun tilasta su wajen karbar addinin musulunci ba da san ransu a lokacin ma'aiki (SAW) babu kamshin gaskiya a cikinsa.

369206