Bangaren Yada Labarai: Wani malamin addinin musulunci dan ahlussunna Mahmud Babayi, ya bayyana cewa dukkanin musulmi Shi'a da Sunna sun kaunar iyalan gidan manzo da Imam Hossein (AS)
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga cibiyar yada addinin muslunci ta lardin Sistan da Baluchestan cewa; daya daga cikin malaman ahlussunna da ke birnin Zahidan Mahmud Bababayi, ya jaddada cewa dukkanin musulmi shi'a da sunna suna matukar kaunar iyalan gidan manzon Allah da Imam Hossein (AS) inda ya bayyana cewa abin da Imam Hosseini ya yi na tsayin daka wajen fuskantar zalunci a Karbala, shi ne babbar abin day a baiwa addinin musulunci damar wanzuwa, domin kuwa da Imam Hossein bai yi haka ba, to da babu abin da zai yi saura a addinin musulunci.
Ya kara da cewa yin aiki da koyarwar ahlul baiti shi ne hakikanin aiki da sunnar ma'aiki.
369396