IQNA

Ci Gaba Da Aikata Ayyukan Sabon Ubangiji Na Nisantar Da Ruhi Imani

Bangaren Cibiyar Kula Da Hubbaren Imam Rida: Ci gaba da aikata sabon ubangiji na nisantar da ruhi daga imani da kuma yarda da kyawawan abubuwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; wani daya daga cikin jami'an da suke kula ayyukan cibiyar kula da hubbaren Imam Rida (Hosseini Ansariyan) ya bayyana cewa; ci gaba da ikata ayyuka sabon ubangiji na nisanta ruhin dan adam daga Imani da ma yarda da kyawawan ayyukan da ke misilta dabi'u na gari, domin kuwa acewarsa sabon ubangiji yana barin mummunan tasiri a cikin ruhin mutum, kuma ci gaba da aikata shi yakan sa ruhin mutum ya mutu, ta yadda zai kasance babu hasken da zai rika daidaita tunanin mutum wajen aikata kyakkayawa ko mummuna.
Ya ce hakan yakan kai mutun ga kiyayya da gaskiya, har ma wani lokaci ya koma yakarta.

369227