Bangaren kasa da kasa: wata Tawaga Ta Musulmin Britaniya Sun Ziyarci Gidan Ajiya Da Maktabar Hubbarin Imam Rida (AS) da cewa al'ummar Iran na bada kulawa da tattalin abubuwa masu kyau na al'adu masu kima.
Reshen Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna a lardin Hurasan net a watsa rahoton cewa: wannan tawaga ta musulmin kasar britaniya ta hada malumman jami'oi,da na kwaloji da ma'aikata da suka tashi takanas domin ziyarar ganewa ido da ziyarar addini a Iran. Idan bayan sun ziyarci gurin ajiyar kayan tarihi da babban dakin litattafai na hubbarin Imam Rida (AS) sun bayyana gamsuwarsu a fili da jinjinawa al'ummar Iran da suka himmatu wajen kula da kiyaye kayan tarihi da al'adu masu kima da hakan yake isar da sako ga sauran al'ummomin duniya.Kuma wannan maktaba na taimakawa musulmi a tsawon tarihi da sauran zamani mai zuwa a nan gaba.
369288