Cibiyar kula da harkokin kkur'ani a iran Ikna ne ta nakalto daga majiyar shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadi Najad cewa:a lokacin abincin dare a lokacin da shugaban ya kai ziyara a kasar Kenya a Otel din Laiko A Nairobi babban birnin kasar ya yi nuni da cewa; dangantaka ta kaunar juna da amfanin bangarori biyu a duk wata hulda ta kasa da kasa it ace za ta kara dongon dangantaka da hulda da kasashen Afrika kuma wannan shi ne tushen mahangar diplaumasiyar Jamhuriyar musulunci a Iran.Ya kara da cewa ci gab da sulhu da tsaro hakki ne na dukan al'ummomi.adalci da girmama dan adam da nuna yan uwantaka da daidaito shi ne ya dace kuma babu wani abu da zai kawo cikas da hana kasashen Iran da Kenya ci gaba.ya kara jaddada cewa A yau lokaci ya yi da kasashe ma'abuta girman kai da danniya da suka yi wa kasashe masu tasowa mulkin mallaka da kuma suke ci gaba da wannan mummunar manufa da siyasa ta zalunci su san cewa lokacin irin wannan siyasa ta zalunci ya kawo karshe kuma a yau lokaci ne na hulda ta gaskiya da dukan bangarori za su amfana.
369382