IQNA

An Watsa maganganun Hikima Na Imam Khomeini ® A Cikin harsunan Karkistan

Bangaren Ilimi : Nasihohi da wakokin Imam Khomeini ® mu'assasin Juyin musulunci a Iran an fassara su zuwa harsunan Karkizistan a matsayin kalamomi na hikima.
Reshen cibiyar kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna dake wannan kasa ta Karkizistan ne ya watsa rahoton cewa: wani littafi day a kumshi shafi 283 na maganganun hikima na Imam Khomeini ® an fassara su da yarukan wannan kasa tare da yadawa a fadin kasar.Karkashin wannan rahoto Bishinbik Kishif marubuci kuma dan jarida a wannan kasa ne ya fassara litafin daga harshen Rasha karkashin umarnin ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci a Iran a wannan kasa.

369147