IQNA

An Bude Kwalejin Hukunce-Hukuncen Musulunci A Kasar Maldive

12:42 - February 28, 2009
Lambar Labari: 1749260
Bangaren kasa da kasa: An bude kwalen farko domin koyar da hukunce-hukuncen addinin musulunci a birnin Male na kasar Maldive.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Maldive News) cewa; an gudanar da bukin bude jami'ar a ranar Alhamis da ta gabata, inda wasu daga cikin manyan baki suka gabatar da jawabai da suka hada da shugaban kasar, wanda ya bayyana cewa bude wannan kwaleji babban ci gaba ne ga kasarsa, domin kuwa a cewarsa kasar tana da kishirwar ilimin addinin musulunci, ya ce yana da masaniya kan wani abu dangane da addinin musulunci, kuma da sannu zai ci gaba da fadada iliminsa kan addinin musulunci
Kasar Maldive kamar kasa ce da ke cikin tsibirin Maldive a kudancin Asia, kuma akasarin mutanen da ke zaune a cikin wannan tsibiri mabiya addinin mslunci ne.
369857




captcha