Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Mohit) cewa; an fara gudanar da gasar ne a bangarori hudu, da suka hada kira'a (tartil) da kuma harda, wanda an raba bangaren hardar zuwa hardar dukkanin alkur'ani mai tsarki, da hardar juzu'i 25, da kuma juzu'i 20, sai kuma juzu'i 15, sai kuma juzu'i 10, da kuma juzu'i 5.
Ministan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar shi ne ya jagoranci bude gasar tare da wakilan wasu kasashen musulmi kimanin 20.
Gasar dai tana samun halartar baki daga kasshen kimanin talatin.
369892