IQNA

Babbar Cibiyar Musulmin Amurka Ta Bukaci Da A Kiyaye Hakkokin Musulmin Kasar

Bangaren kasa da kasa. Babbar cibiyar Musulmin kasar Amurka ta bukaci babbar kotun kolin kasar da ta dauki matakan da suka dace wajen kiyaye hakkokin musulmin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (PR Newswire) cewa; cibiyar musulmin Amurkan ta aike da wata wasika zuwa ga sabon babban alkalin kotun kolin kasar, inda ta bayyana masa cewa musulmin kasar sun fuskancin matsaloli da dama, musamman a cikin 'yan shekarun da suka gabata, sakamakon parpaganda da aka yi ta yi domin bata sunan addinin musulunci, cibiyar ta bukaci babban alkali ya taka rawa wajen ganin an kiyaye hakkokin musulmi a kasar Amurka.
A bangare guda kuma cibiyar ta soki lamirin 'yan majalisar da suka bukaci da a nuna fim din fitina a congress da wani dan kasar Holand ya shirya, da nufin tozarta addinin musulunci.

369884