Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Nasij) cewa; jami'ar Azhar za ta dauki nauyin gudanar da taron kusanto dac mazhabobin Musulunci, da nufin fuskantar parpagandar da ake yi kan addinin Musulunci da nufin bata surarsa a idon sauran al'ummomin duniya wadanda ba musulmi ba, kmaar yadda taron zai tabo batun jingije duk wani rikon kankamo kan mazhaba da daina kafita wasu, da hada kai a matsayin mabiya addini guda, tare da girmama juna, da kuma girmama ra'ayin kowa.
An gudanar da irin wannan taro a karo na goma sha biyu a a cikin shekara ta 2002, inda mahalarta taron suka yi bahasi kan batun banbancin fahimta kan wasu mas'aloli tsakanin mazhabobi, da kuma wasu batutuwa da suke komawa zuwa ga tarihin Musulunci, da nufin samar da fahimtar juna tsakanin al'ummar musulmi.
370233