IQNA

Tarayyar Turai Na Goyon Bayan Hadin Kai Tsakanin Kungiyoyin Palastinawa

11:57 - March 01, 2009
Lambar Labari: 1749674
Bangaren kasa da kasa: Kungiyar Tarayyar Turai ta nuna cikakkaen goyon bayanta ga duk wani yunkuri na samar da hadin kai tsakanin kungiyoyin Palastinawa.
Kmafanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Islam Online) cewa; a wata ziyara da babban jami'i mai kula da harkokin wajen tarayyar turar Havir Solana ya kai zirin Gaza a jiya Juma, ya bayyana cewa tarayyar turai na goyon samun hadin kai tsakanin kungiyoyin palastinawa, da hakan ya hada da Hamas da kuma Fatah, ya kara da cewa samun hadin kai tsakanin kungiyoyin Palstinawa shi ne babban abin da zai ba su damar zama tsintsiya daya madaurinki daya wajen daukar matakai da suka da su, kuma hakan zai bayar da dama wajen samu a cimma nasara a tattaunawar sulhu da zaman lafiya da kafa kasar Palastinu mai cin gishin kanta.
Havir Solana ya bayyana cewa; babbar manufar ziyarar tasa ita ce gane wa idanunsa barnar da hare-haren Isra'ila suka jawo wa al'ummar gaza.

370157










captcha