IQNA

An Fitar Tare Da Yada Littafin Maudu'an Kur'ani A Kasar Rasha

10:19 - March 02, 2009
Lambar Labari: 1750281
Bnagaren Kur'ani: An fitar tare da yada littafin maudu'an kur'ani a kasar Rasha a cikin harshe rashanci, bisa kokarin da bangaren yada al'adun Iran ke yi a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada al'adun Iran a kasar Tailand cewa, marubucin littafin (Shakir Ahmad) ya yi amfani da salo mai sauki wajen bayyana ma'anonin ayoyin kur'ani, ta yadda koya zai iya fahimta cikin sauki.
Marubucin ya kawo ayoyi da suke fadakar mabiya addinan yahudanci da nasara gami da musulmi kan samuwar ubangiji madaukakin sarki, tare da yi musu hannunka mai sanda.
Madaba'antar (Iliya) ce ta buga littafin a cikin shafuka 384.

370842

captcha