Bangaren Rahoto: Shugaban reshen jami'ar Mostafa (SAW) a kasar Afghanistan, ya bayyana cewa yanzu haka suna da daliban a bangaren ilimomin kur'ani sama da dubu goma a rassan jami'ar da ke sassa daban-daban na kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga banagren yada labarai na cibiyar ilimi ta Hauza cewa; daga cikin ayyukan da jami'ar take gudanarwa a rassanta da ke kasar Afghanistan har karfafa ilimin kur'ani, da hakan ya hada bude cibiyoyin nazarinsa, da kuma dakunan karatu, gami da shirya gasa a sassa daban-daban na kasar.
Majiyar ta kara da cewa; an shirya gudanar da wani taron bayar da horo ga malaman da za su ci gaba da gudanar da ayyukan koyarwa a rassan jami'ar, an kuma gudanar da taron bayar da horon ne ga malamai 100 a birnin Kabul fadar mulkin kasar.
370673