IQNA

Dubun Dubatar Masu Ziyara Ne Ke Ci Gaba Da Isa Hubbaren Abdul'azim (SA)

Bangaren Zamantakewa: Tun bayan kamawar watan Rabi'ul Awwal, masu ziyara suke ci gaba da yin cincirindo a hubbaren Abdulazim(SA) da Sayyid Abdulkarim (SA) domin gudanar da ayyukan ziyara a wadannan wurare masu tsarki.
Kamfanin dillancin Ikna ya habarta cewa; tun bayan da watan Rabiul Awwal ya kama, dubban masu ziyzra ke ci gaba da isa wadannan wurare masu tsarki, domin gudanar da ayyukan ziyara, kasantuwar watan Rabi'ul Awwal wata ne mai madaukakiyar daraja da matsayi na musamman a wajen al'ummar musulmi.
A cikin wannan wata ne manzo Allah (SAW) ya yi hijira daga Makka zuwa Madina, a cikinsa ne aka haifi shi, kuma cikinsa ne aka haifi Imam Sadiq (AS) a cikinsa ne kuma manzon Allah (SAW) ya auri Khadija, a cikinsa ne kuma imamancin Imam Mahdi (AS) kuma cikinsa ne Mu'awiyya Dan Abu Sufyan ya halaka. Wadannan nan dai na daga cikin muhimman abubuwa da suka faru a cikin wannan wata mai alfarma.

370813