IQNA

Za A Gudanar Gasar Kur'ani Da Hadisan Annabi A Kasar Oman

10:08 - March 02, 2009
Lambar Labari: 1750285
Bangaren kasa da kasa: A cikin wannan wata ne za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki da hadisan annabi a jami'ar (Rustaq) da ke kasar Oman.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-shabibah) da ake bugawa a kasar Oman cewa; za a gudanar da wannan gasa ne bias kulawar jami'ar Rustaq, kuma dalibai da dama daga sassa daban-daban na kasar ne za su shiga gasar.
Daga cikin bangarorin da za a gudanar da gasar kansu hard a karatun kur'ani, da kuma tajwidi, wato ka'idojin karatun kur'ani, da kuma hardar dukkanin kur'ani, sai kuma hardar juzu'I na tara, goma, sha daya, sha biyu, gami da sharhin hadisan manzon Allah guda talatin.
Kwamitin kula da shirya gasar ya sanar a tab akin sakatarensa cewa; babbar manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce karfafa daliban kasar wajen mayar da hankali kan karatun kur'ani da hardarsa da kuma kyautata tajwidi, gami da sanin hadisan manzon Allah, ta yadda hakan zai ba matasa dammar sanin addini.


370811


captcha