Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren dalibai sojin sa kai na (Basij) na jami'ar Imam Sadiq (AS) cewa; daliban sun rubuta wata wasika zuwa ga ministan shari'a na kasar Iran, da a cikin suka kirayi ministan da ya taka rawa wajen ganin an sake farfado da kurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 3379, da aka fitar a ranar 10 ga watan Nuwamban 1970 wanda ya bayyana ayyukan Haramtacciyar Kasar Isra'ila a kan al'ummar Palastinu a matsayin ayyuka na nuna wariya, amma sakamakon goyon bayan da Amurka take baiwa gwamnatin yahudawan sahyuniya aka manta wannan kudiri.
A bangare guda kuma sun bukaci da gyrfanar da gwamnatin yahudawan sakamakon ayyukan yaki da ta aikata na tsawon kwanaki 22 a kan al'ummar Gaza marassa kariya.
370875