IQNA

Komitin Agaji Na waliyul Asr (AJ) Ya Bude Cibiyar Taimakawa Musulmin Bankuk

Bangaren siyasa da zamantakewa: Komitin bayar da agaji na Waliyul Asr (AJ) ya bude cibiyarsa ta taimakawa talakkkawa a birnin Bankuk fadar mulkin kasar Tailand.
Daga yankin kudu maso gabacin Asiya ne cibiyar da ke kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Sheikh Muhammad Na'im mai bada salla a masallacin Sahibul zaman (AJ) a birnin Bankuk kuma da ke karatu a jami'ar almustapha (SWA) al'alami da ke birninQum ya bayyana cewa: wannan komitti daga shekara ta 1428 hijira kamariya ne ya fara gudanar da aikin taimakawa musulmi marassa karfi talakkawa masu bukatar a agaza masu a wannan birni.Ya kara da cewa a halin yanzu wannan komiti yanada mambobi 193 kuma taimakwa talakkawa wani abu ne da ked a matukar muhimmanci a musulunci kuma a dayan bangare suna taimakwa marassa lafiya a asibitoci a wannan birni da sauran bangarori da komitin ke agazawa al'umma.

369847