IQNA

Yaduwar Musulunci Wani Babban Hadari Ne Ga Gwamnatin Yahudawanci

10:39 - March 02, 2009
Lambar Labari: 1750416
Bangaren siyasa da zamantakewa: Yaduwa da ci gaban Musulunci da Iran babban hadari ne ga gwamnatin HKI.
Cibiyar da ke kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; wakilin yankin Sari a majalisar shawarar musulunci a Iran Murtada Ni'imat Zade kuma mataimakin shugaban kungiyar kare al'ummar palasdinu a lokacin bukin kasuwar baje koli itatuwan zeitun ya bayyana cewa: Ruhin musulunci ne ya karfafawa al'ummar gaza cin nasara kan gwamnatin zaluncin ta yahudawan sahayoniya. Ya kara da cewa: yakin Gaza yanada mahanga guda biyu ta farko ta'adfdancin HKI kan al'ummar Palasdinu a Gaza sai kuma bangare na biyu tsayin daka da gwagwarmayar al'ummar Palasdinu da fuskantar ma'abuta girman kai da cin nasara a kansu.saboda haka ci gaba da yaduwar musulunci babbanhadari ne ga HKI.

371037
captcha