IQNA

Al'ummar Birnin Worcester Na Birtaniya Na Goyon Bayan Al'ummar Gaza

13:23 - March 03, 2009
Lambar Labari: 1751087
Bangaren kasa da kasa: Alen Aimos mamba a majalisar birnin Worcester ta bayyana cewa; za a saka wa birnin suna dan uwan Gaza, domin nuna goyon bayan ga al'ummar Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Sana cewa; Alen Aimos ta bayyana hakan ne a wata zantawa da ta hada ta da tashar talabijin ta hudu ta kasar Birtaniya, inda ta bayyana cewa bisa la'akari da matsanancin zalunci da al'ummar Gaza suke fuskanta daga Isra'ila, majalisar Birnin ta kudiri aniyar kiran birnin da suna dan uwan Gaza, domin nuna goyon baya ga al'ummar yankin, musamman wadanda suka rasa iyayensu da 'yan uwansu da 'ya'yansu, da kuma wadanda suka samu munan raunuka sakamakon hare-haren kare dangi da Isra'ila ta kai kansu.
Ta kara da cewa yanzu mambobin majalisar birnin Worcester da ke yammacin birnin London na nan suna tattauna wannan batu, da zaran sun amince da hakan kuma za a sanar.

371457

captcha