IQNA

Za A Baje Kolin Kayayyakin Fasahar Hannu A Birnin Lahore Na Pakistan

Bangaren al'adu da fasaha: Za a gudanar da baje kolin kayyakin tarihi da fasaha a birnin Lahore na kasar Pakistan, domin murnar haihuwar manzon rahma (SAW) da kuma makon hadin kai.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga majiyoyin ofishin yada al'adu na kasar Iran da ke birnin Lahore cewa; za a gudanar da baje kolin ne a birnin, kuma zai samu halartar masana da masu gudanar da ayyukan fasahr hannu daga sassa daban –daban na kasar Pakistan, inda za su nuna irin baiwar da Allah ya yi musu.
Daga cikin abubuwan da za a nuna hard a zane-zane da ke alamta musulunci, da kuma wasu ayyukan fasaha kamar sassaka wasu abubuwa daga itace, ko zanen dutse da dai sauransu. Wadanda suka gudanar da ayyukan fasahar, sun samu horo ne daga ofishin kula da al'adu na Iran da ke birnin Lahore.

371469