A wata zantawa da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran Ikna shugaban bangaren kula da al'adu da tarbiya na jami'ar Mostafa a birnin Qom Mohammad Hojjatiyan, ya bayyana cewa yanzu haka jami'ar na nan ta shirin fara aiwatar da dukkanin shirye-shiryenta kan harkokin alkur'ani a kasar Syria, kuma za a gudanar da shirin ne ta hanyar bude ajujuwa.
Ya ce daga cikin abin da shirin zai kunsa har da koyar da karatun kur'ani da harda, da kuma koyar da ma'anonin kur'ani, tare da shirye gasa lokaci zuwa lokaci.
Ya kara da cewa shirin zai fara ne da daukar dalibai 60 wadanda za su mayar da hankali kan lamurran kur'ani a Syria, kamar yadda a cikin shirin ne kuma za a rika bayar da horo ga malan da za su rika koyarwa.
370547