Bangaren siyasa da zamantakewa: Za a gudanar da taron dalibai da limamai da suka kammala karatu a birnin Qom a ofishin kula da al'adu na Iran da ke birnin Bankuk na kasar Thailand.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga majiyoyin ofishin kula da al'adu na Iran da ke birnin Bankuk na kasar Thailand cewa; za a gudanar da taron dalibai da limaman juma'a na kasar Thailand wadanda suka kammala karatunsu a cibiyar ilimi ta Hauza da ke birnin Qom, kuma wakilin jagoran juyin juya halin musulunci a Iran a kasashen Meyanmar, Bangaladesh da Thailand (Ayatollah Shahrakhi) shi ne zai jagoranci gudanar da taron.
A wannan taro malamin zai gabatar da bayani kan tarihin rayuwar Imam Hassan Askari (AS) da kuma sauran maudua'I na kaywawan dabi'u da dai sauransu, kamar yadda dalibai da limaman juma'a da za su halarci wurin za su tattauna a kan batutuwa daban-daban na mas'alolin shari'ar msulunci.
371491