Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren da ke kula da harkokin hulda da jama'a a babbar kotun koli ta Tehran cewa; an gudanar da bincike kan jami'an Isra'ila 15 kuma bisa ka'idoji na 146, da 147, na hukumar 'yan sanda ta kasa, an same su da laifin karya dokokin da suka shafi kare fararen hula, wanda kuma bisa wadannan ayoyin doka wanda ya aikata hakan hakkin hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa Interpol net a kame shi. Kuma tuni a ka mika sakamakon wannan bincike gag a hukumar wadda ke da wakilcin kasashe sama da 180 daga sassan duniya.
Sunayen kuwa su ne: 1- Ehud Olmert 2- Ehud Barack 3- Tzipi Livni 4- Raualov Gabi 5- Aido Neyohastan 6- Yuwa Galant 7- Ran ashro 8- Amos Badlin 9- Arian kohen 10- Yuwa Markhay 11- Yegal Asloyek 12- Avey Blatt 13- Avey Blad 14- Hatzy Haloy 15- Tamer Tester.
Wadannan mutane suna da hhanu a yakin da aka fara kan Gaza daga ranar 27 ga Disemban 2008, , an kasha fararen hula palastinawa sama da 1285, da suka hada da mata 111, da yara 281, da rushe gidaje 2400.
Bisa binciken da aka gudanar wadannan mutanen dole su gurfana gaban shari'a.
371404