IQNA

An Fara Taron Sake Gina Gaza A Sharm Al-shekh

13:14 - March 03, 2009
Lambar Labari: 1751101
Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da taron sake gina Gaza Sharm Al-sheikh na kasar Masar, tare da halartar bangarori daban-daban na duniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Nasij) cewa: Shugaban kasar ta Masar shi ne ke jagorantar gudanar da taron, inda ya bude da jawabinsa na farko. Bayanin ya ce kimanin ministocin harkokin waje 71 ne daga kasashen duniya suke halartar taron, gami da shugabannin wasu kasashen, kamar yadda tawagar kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta OIC ke halartar taron, gami da kwamitin bangarori da yahada Majalisar Dinkin Duniya, Amurka Rasha da Kungiyar tarayyar turai ke halartar taron.
Haka nan kasashen yankin tekun fasha suna halartar taron domin nuna shirin da suke da shi na sake gina Gaza, bayan da suka kammala nasu taron kwana daya rak kafin gudanar da taron na Masar, inda suka hada makudan kudi da nufin sake gina Gaza.

371501




captcha