IQNA

Fara Gasar Alkur'ani Ta Kasa Da Kasa A Kasar Katar

15:24 - March 03, 2009
Lambar Labari: 1751216
Bangaren kasa da kasa: a ranar litinin da ta gabata ce aka fara gasar Alkur'ani ta kasa da kasa a birnin Doha fadar mulkin kasar Katar.
Bayan ta nakalton daga jaridar Peninsula da ake bugawa a kasar Katar ,cibiyar kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: a wannan gasar ta Alkur'ani kimanin masana alkur'ani 20 ne daga kasashen Maleishiya,Pakistan,Turkiya,Masar,Palasdinu,Maroko ,Amerika,Jodan,Indonosiya da Jamus suka halarta tare da sauran takwarorinsu na komitin tuntubar juna a tekun Fasha.A wannan taro masana za su yi nazari kan ayoyin alkur'ani da hadisai da kuma ci gaban ilimi na zamani mmuhalli da yadda za a kiyaye dabi'u da kayan tarihi da na hannu tare da aiki da majalisar dinkin duniya suna daga cikin muhimman abubuwa da mahalarta taron za su yi nazari da masanyar ra'ayoyi kansu a cikin kwanaki uku .

371497

captcha