IQNA

Uglu Ya Bayyana Farin Cikinsa Da Tattaunawa Tsakanin Kungiyoyin Palasdinu

Bangaren kasa da kasa: Ikmaldine Ihsan Uglu babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya gamsu da tattaunawa tsakanin kungiyoyin Palasdinu a Masar.
Bayan ta nakalto daga OCI cibiyar kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Ihsan Uglu ya yaba da kokarin da gwamnatin Masar take yi na samara da kusanci tsakanin kungiyoyin Palasdinu da hakan zai kais u ga kafa gwamnatin hadin kan kasa.Kuma tuni kasashe da gwamnatoci gami da kungoyin masu zamankansu da kuma al'ummomi ma na bayyana ra'ayoyinsu kai tsaye da farin cikinsu kan haka.Tare da fatar gamin masu shiga sharo ba shanu da bata rowan miya bas u coma bakinsu.

371578