Kamfanin dillancin labaran Ikna daga birnin Isfahan ya habarta cewa; a wani taro da aka gudanar a babban ofishin gwamnan lardin, mataimakin gwamnan kuma shugaban cibiyar kula da tsaida salla reshen Isfahan (Reza Jadidi) ya bayyana cewa; masallatai ba wurare ne kawai na yin salla ba, a wurare na gudanar da dukkanin ayyukan ibada, haka nan kuma wurare ne na gudanar da ayyuakan wayar da kai bayar da horo, wurare ne na bahasi kan lamurran siyasa, al'adu, fasaha, rayuwar zamantakewa , adabi da dai sauransu.
Ya ce idan haka ne kuwa, to masallatai wurare ne da za a iya yin amfani da su wajen bayyana sahihan al'adu da dabi'u na musulunci, tare da tantance al'adu da dabi'u da suka yi karo da koyarwar addinin musulunci.
Ya ce daga cikin irin kokarin da reshen cibiyar kula da tsaida salla reshen Isfahan ke yi, a cikin 'yan lokutan nan an bude wuraren salla kimanin 600.
372181