A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labarab Ikna da wani jami'i a ma'aikatar kuka da harkokin kur'ani ta Iran (Ali Mogni) ya bayyana cewa; za a gudanar da taron ne a karo na biyu, wanda zai samu halarta mutane kimanin 100 daga sassa daban-daban na kasar, inda wasu daga cikinsu za su gabatar da makalolinsu kan fannoni daban-daban da alkur'ani ke koyar da mutum tarbiya tare da shiryar da shi zuwa ga sahihin tafarki na rayuwa.
Ya kara da cewa; taron zai dauki kwanaki biyu a jeer ana gudanar da shi a masallacin jamkaran da ke Qom, kuma tuni aka gudanar da dukkanin shirye-shiryen da suka kamata domin ganin taron ya kayatar, musamman ma ganin cewa mutane da da yawa ne za su halarci wurin taron a matsayin 'yan kallo daga ko'in cikin fadin kasar.
379426