Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren kula da harkokin kasashen waje a majalisar shawara ta Iran cewa; a wata zantawa da ta hada wakilan bangarori marassa rinjaye a Iran a majalisar shawara ta Iran, da shugabar kwamitin kula harkokin waje a majalisar dokokin kasar Danmark a zauren majalisar shawara da ke birnin Tehran, sun tabbatar mata da cewa babu matsalar kyamar addinai ko marassa rinjaye a Iran, kamar yadda wakilan mabiya addinan yahudawa da na kiristanci suka tabbatar.
A nata bangaren shugabar kwamitin kula da harkokin kasashen ketare a majalisar kasar Danmark, ta fadi a zauren majalisar shawara ta Iran cewa hakika babu kyamar addinin yahudanci ko kiristanci a Iran.
372093