Bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta MAP ,cibiyar kula da harkokin Alkur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; wannan gasar hardar Alkur'ani an shirya tane da nufin tunawa da zagayowar ranar haifuwar fiyayyan halitta Muhammadu dan Abdallah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayansa.Ma'aikatar kula da sha'anin addini a wannan kasa ta Marokko ta bayyana cewa wannan gasar tamkar ciko ne na babbar gasar Alkur'ani da za a gudanar a ranekun 14 da 15 ga watan Oktoban a Marokko.
372308