IQNA

Iran Na Karkashin Koyarwa Ta Gadir Da Yada Wannan Manufa A Kasa Da Kasa

Bangaren kasa da kasa: kafa cibiyoyin gadir a kasashen waje yana daga cikin ayyukan wannan babban cibiya a kasashe 19 na duniya.
Cibiyar kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: a zauren da za a gudanar da taron uwar cibiyar gadir ta kasa da kasa Malam Hasan Malik Muhammadi babban darektan wannan cibiya ta kasa da kasa ya bayyana cewa; ya zuwa yanzu sunada ofisoshin goma sha tara a kasashe daban-daban kamarsu Tunusiya,Maroko,Kanada,Ostriya, Holand,Beljik kuma a nan gaba za su bude ofishinsu a wasu kasashe goma. Kuma daga cikin ayyukan da cibiyar Gadir ke gudanarwa akwai buga littafai da suka shafi Imam Ali (AS) da lakur'ani mai girma.

372217