IQNA

A Taron sake Gina Gaza A Masar An Jaddada Bude Mashigar Rafah

14:07 - March 04, 2009
Lambar Labari: 1751725
Bangaren kasa da kasa: mahalarta taron na gurin shakatawa na sharmun Sheikh a wannan taro na kasa da kasa kan tara kudaden sake gina yankin Gaza sun bukaci HKI da ta bude mashigar Rafah cikin gaggauwa domin isar da abinci da magunguna a yanki.
Cibiyar kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ce bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Masar Sana ta watsa rahoton cewa: mahalarta taron na gurin Shakatawa na Sharmun Sheikh a cikin bayanin bayan taro sun jaddada wajibcin gwamnatin HKI ta bude mashigar Rafah kuma dole ta kiyaye dokokin kasa da kasa da ta canja matakin kai wad a lalata guraren kasuwanci da na fararen hula. A wani bangare na bayanin bayan taron kasa da kasa kan sake gin aGaza sun bukaci HKi da ta ba su damar isar da abubuwa na farko da ake bukata kafin fara sake gina gurare da gidajen da ta ruguza. A wannan taron kimanin dala biliyan hudu da miliyon dari hudu da tamanin aka yi alkawalin bayarwa.

372164
captcha