IQNA

Taron Wuni Daya Kan Ta'addanci Da take Hakkokin Kasa Da Kasa A Gaza

14:06 - March 04, 2009
Lambar Labari: 1751726
Bangaren kasa da kasa: A ranar talata ce da safe a birin Tehran an gudanar da taron karawa juna sani na wuni daya kan ta'addanci da take hakkokin kasa da kasa da HKI ta tabka a Gaza.
Cibiyar da ke kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ce ta watsa labarin cewa a safiyar jiya talata ce aka gudanar da taron karawa juna sani na wuni daya kan rashin tausayi n akarshe da aka nunawa dan adam da kuma take hakkokin kasa da kasa da gwamnatin HKI ta tabka a yankin Gaza kuma an gudanar da wannan taro ne a zauren taro na otel din Istiglal inda masu kare hakkokin dan adam da loyoyi da alkalai da malummai suka halarta kuma wanda ya fara gabatar da jawabi a gurin taro shi ne sheikh dari najaf Abad babban alkalin kasa a Iran sai kuma Larjani shugaban hukumar kare hakkin dan adam sai kuma Ahmad Jibril babban sakataren kungiyar Palasdinu mai neman yanci da Mahmud Jawad suna daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai a gurin.

372285
captcha