Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Islam online) cewa; malaman kasar Masar sun fitar da wani bayani da a cikinsa suka bayyana rashin amincewarsu da duk wani batun cire wasu daruusa da ke sukar wasu addinai, bayanin ya ce littafan musulmi ba su bukatar a cire wani abu daga cikinsu, domin babu sukar wasa addinai ko mabiyansu a cikin littafan musulmi. Bayanin ya ce littafan da ake koyar da su a makarantun kasashen turai dai su n eke bukatar kwakwarima, domin kuwa su ne suke sukar addinin musulunci da mabiyansa.
A zaman da wakilan jami'ar Azhar da na fadar Vatican suka gudanar a kwanakin baya ne suka amince kan cewa a cire duk wasu darussa da suke sukar addinai a cikin littafan darasi na kasashen musulmi da kirista.
372825