Bangaren kasa da kasa: Wadanda suka gudanar da zama kan batun hare-haren ta'addancin da Isra'ila ta kai kan al'ummar Gaza tare da cin zarafin dan adam a yankin, sun fitar da bayani da ke tabbatar da cewa Isra'ila ta aikata laifukan yaki.
Kamfanin dillancin labarn Ikna ya habarta cewa; wadanda suka gudanar da taro kan keta hurumin dan adam a Gaza sun bayyana a cikin bayanin bayan taronsu cewa; Isra'ila ta aikata laifukan yaki kan al'ummar Gaza, a kan haka dole a gurfanar da jami'anta da suke da hannu kai tsaye wajen aikta wannan aika-aika kan fararen hular Gaza.
Bayanin ya bayyana cewa harin na Isra'ila kan fararen hular Gaza ya yi karo da dukkanin dokoki na kasa da kasa, kamar yadda ci gaba da killace zirin Gaza ya ke tabbatar da cewa har yanzu Isra'ila bat a kawo karshen yakinta kan al'ummar gaza.
Bayanin ya kara da cewa dole kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya safke nauyin da ya rataya kansa wajen gurfanar da wadanda suka aikata laifukan kisan kiyashi kan fararen hula a Gaza. Kamar yadda bayanin bayan taron ya jaddada cewa hakkin al'ummar Palastinu ne su yi gwagwarmaya kwatar 'yancinsu.
372764