Bangaren kasa da kasa: Gwamnatin kasar Algeria ta sanar da dokar hana bayar da fatawoyin addini a gidajen talabijin din kasar, sakamakon yawaitar gidajen tabijin da ke bayar da fatawoyin addinin ba bisa ka'ida ba a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Liberte- algerie) cewa; hukumar da ke kula da harkokin addinin musulunci a kasar Algeria ta bayyana cewa; bisa la'akari da yawaitar tashoshin talabijin a kasar da suke bayar da fatawowin addini ba tare da cikakkiyar masaniya kan addini ba, wannan ya sanya jami'an hukumar kiran wani zaman taron gaggawa domin tattauna hanyoyin da za a shawo kan lamarin, inda suka cimma matsaya kan hana bayar da duk wasu fatawowin addini ta hanyar gidajane tabijin, a maimakon haka cibiyoyin addini da aka san da zamansu a hukumance gami da makarntun addini da ke karkashin sanannun malamai, su ne suke da alhakin bayar da fatawa a kasar.
373632