Bangaren kasa da kasa: Masu zane-zanen ginin cibiyar musulunci ta Arsenal sun baje kolin ayyukan da suka gudanar kan hakan a birnin Paris na kasar faransa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na 20 minutes cewa; an baje kolin ne a wani wuri da ake gudanar da baje kolin kayayyakin ilimi da fasaha a birnin Paris, inda kungiyoyin musulmi biyar da suke gudanar da ayyukan hadin gwiwa domin gina babbar cibiyar al'adun musulunci a Faransa, suka baje zane-zanen ginin cibiyar, wanda ake sa ran kammala gininta a cikin shekara ta 2010, kuma cibiyar za ta kunshi manyan rassa biyu ne, daya a babban titin (Stephenson) yayin da dayan reshen kuma za a gina shi ne a titin (polenceau)
Kungiyar musulmin birnin Lyon su ne suka mika zane-zane masu kayatarwa fiye da sauran kungiyon, inda ake sa ran yin amfani da su wajen gina rassa cibiyar guda biyu.
373613