Bangaren siyasa: Mai baiwa jagoran juyin juya halin musulunci a Iran shawarwari kan harkokin siyasa Ali Akbar Wilayati, ya bayyana cewa rarraba tsakanin shi'a da Sunna na kawo rauni a cikin lamarin musulmi.
A wata zantawa da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran Ikna, mai bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ga jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ali Akbar Wilyati, ya bayyana cewa a ko da yaushe hadin kai shi ne mabudin cin nasara da ci gaban kowane irin lamari, kamar yadda ya zama wajibi al'ummar musulmi su hada kansu wuri guda, tare da ajiye banbance-banbancen fahimta na mazhaba a tsakaninsu, domin kuwa duk wani sabani tsakanin shi'a da sunna ba shi ne abin day a hada bangarorin biyu ba, babban abin da ya hada su shi ne addinin musulunci, kuma duk wata rarraba tsakaninsu za ta raunana karfin musuluncin ne, domin kuwa dukkansu musulmi ne, sabanin fahimta kan wasu mas'aloli na gefe ba zai kore musuluncin daya bangaren ba.
Wilayati ya jaddada wajabcin hadin kai tsakanin dukkanin musulmi, tare da mayar da hankali kan muhimman batutuwa da suke ci wa duniyar musulunci tuwo a kwarya maimakon ruruta wutar sabani.
373607