Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a ranar Alhamis da ta gabata ce aka kawo karshen taron da majalisar shawara ta Iran ta shirya don nuna goyon baya ga al'ummar palastinu, wanda ya samu halartar wasu daga cikin shugabannin majalisun dokoki na kasashen musulmi, da kuma masana daga kasashen duniya sama da 80.
A cikin bayanin bayan taron da mahalarta taron suka fitar, sun jaddada wajabcin taimaka ma al'ummar palastinu, tare da nuna goyon baya gare su, musamman al'ummar Gaza wadanda suke cikin halin neman taimako daga 'yan uwansu musulmi, inda suka yi Allawadai da matakin da wasu bangarori suka dauka na nuna goyon baya ga ta'addancin Isra'ila kan fararen hulamarassa kariya, inda daruruwan kananan yara da mata suka rasa rayukansu wasu dubbai kuma suka jikkata.
373449