Ali Rida Kubasji kwararrai kuma shugaban kula da yada ilimi da tarbiya a yankin kuduncin Khurasan a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran ya bayyana cewa: a cikin wannan kudi Riyal biliyan daya ,miliyan 188 da dubu 511 da 600 zai shafi bangaren gina Gaza yayinda wasu biliyan daya da miliyan 635 da kuma 950 za a taimakawa iyalai.Ya ci gaba da cewa: har yanzu ana ci gaba da tara kudaden taimakawa al'ummar ta Palasdinu inda mutane ke farin cikin taimakawa yan uwansu musulmi da aka zalunta.
373330