Bangaren kasa da kasa; Sheikh Mostafa Isma'il a lokacin rayuwarsa ba ya karbar lada a matsayin sharadin karatun kur'ani, kuma ya kasance yana yin hani kan hakan saboda kyawawan dabi'unsa da kaskantar da kansa.
An gudanar da tarukan tunawa da shahararren malamin nan makarancin kur'ani na kasar Masar Sheikh Mostafa Isama'il, dangane da irin gudunmawar da ya bayar ta fuskacin karatun kur'ani a duniya, wanda har inda yau take makaranta kur'ani ba su gushe ba suna amfana da salonsa wajen karatun kur'ani.
An haifi malamin ne a kauyen (Maitul Gazal) da ke karkashin gundumar (Tanta) a kasar Masar a cikin shekara ta 1905, ya hardace kur'ani baki daya tun yana dan shekaru 12 da haihuwa, ya shahara a kasar baki daya ta fuskacin karatun kur'ani da kyautata kira'a, inda akan gayyace shi domin taruka da karatun kur'ani tun yana dan shekaru goma sha wani abu da haihuwa. Sheikh Mohammad Raf'at ya tasirantu matuka da sheikh Mostafa Isma'ila, wannan ne ma ya sanya shi yin amfani da salon kira'arsa wanda shi ma ya shahara da shi a duniyar musulmi.
373765