IQNA

Al-taruti: Kira'ar Mostafa Isma'il Ba Ta Kebantu Da Wani Zamani Ba

17:04 - March 08, 2009
Lambar Labari: 1753093
Bangaren kasa da kasa: Mostafa Isma'il ya kasance malamin kur'ani, wanda ya assasa makaranta da ta amfanar da duniyar musuli da ba a gushe ba ana ci gaba da amfana da ita a fagen karatun kur'ani mai tsarki.
An haifi Mostafa Isma'il a kauyen Maitul Gazal da ke cikin yankin Tanta a kasar Masar, ya tashi cikin yanayi da ya bashi dammar fara hardar kur'ani tun yana karamin yaro, inda ya hardace kur'ani baki daya tun yana dan shekaru goma sha biyu da haihuwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna, kafar yada labarai kan sha'anin kur'ani guda daya tilo da take yada labarai a cikin yaruka 20 na duniya, ta gudanar da hirarraki da manyan malaman addini da masana da kuma makaranta alkur'ani na cikin gida da waje dangane da irin rawar da shehin malamin ya taka ta fuskacin yada ilimin kur'ani da kira'arsa a duniyar musulmi. Dukkanin malaman da suka bayyana ra'ayinsu kan hakan sun tabbatar da cewa Mostafa Isma'il ya kasance mutum ne mai matukar kokari tare da damuwa da sha'anin kur'ani, kuma ya karar da rayuwarsa baki daya wajen yi wa kur'ani hidima.

373680

captcha