IQNA

Mostafa Isma'il Ya Kebanta Da La'akari Da Ma'anar Aya A Yayin Kira'a

17:02 - March 08, 2009
Lambar Labari: 1753094
Bangaren kasa da kasa: Daga daga cikin muhimmman abubuwan da sheikh Mostafa Isma'il ya kebanta da su a lokacin da yake karatun kur'ani shi ne mayar da hankali ga ma'anonin ayoyin da yake karantawa.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da wani fitaccen malami kuma makarancin kur'ani na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE (Abdolaziz Ali Al-husni) ya bayyana cewa; hakika sheikh Mostafa Isma'ila yana wasu siffofi wadanda ya kebanta da su, daga cikin irin wadannan siffofi kuwa har mayar da hankali ga ma'anar ayoyi a lokacin da yake karatun kur'ani mai tsarki, inda yakan tsaya a kan aya domin yi la'akari da ma'anarta kafin ya wuce zuwa ga aya ta gaba.
A bangare guda kuma ya yi fice ta fuskacin kyautata sauti a lokacin da yake karatun kur'ani mai tsarki, kamar yadda da dama daga ciki makaranta a duniyar msulmi suke bin salon karatunsa wajen karanta kur'ani.
Ya kasance malami ne daga cikin malamai da ake komawa zuwa gare su tafuskacin karatun kur'ani, kamar yadda ya koyar da wasu manyan malami da suka shahara aduniya musulmi ta fuskacin karatun kur'ani, daga cikinsu kuwa hard a sheikh Abdulbasit Abdulsamad, da kuma malamai irin su shikh Munshawi, da dai sauran malamai da suka shahara a kasar Masar da ma duniya baki daya.

373715


captcha