IQNA

Hukuncin Kotun Duniya Kan Albashir Kautar Da Hankula Ne Daga Ta'asar Isra'ila

17:01 - March 08, 2009
Lambar Labari: 1753095
Bangaren siyasa: Shugaban majalisar shawara ta Iran Ali larijani ya bayyana cewa; sammacin da kotun manyan laifuka ta duniya kan shugaba Albashir, wata yaudara ce ta dauke hankulan al'ummomin duniya daga ta'addancin Isra'ila kan al'ummar Gaza.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa; a wata ganawa da ta hada shugaban majalisar dokokin Iran Ali Larijani da shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir a yammacin jiya a birnin Khartum na kasar Sudan, Ali Larijani ya bayyana cewa babbar manufar kotun manyan laifuka ta duniya dangane da fitar da sammaci kan Shugaban Sudan, ita janye hankulan al'ummomin duniya daga ta'asar da Isra'ila ta aikata kan al'ummar Gaza, inda duniya ta sheda ayyukan yaki da yahudawan sahyuniya suka aikata kan daruruwan kananan yara da mata, tare da rushe dubban gidaje da cibiyoyi, gami da makarantu da masallatai da dai sauransu.
Larijani ya ce Iran tana goyon bayan al'ummar Sudan wajen watsi da wannan hukunci na siyasa, da kasashen duniya masu girman kai ke neman yin amfani da shi wajen yin shishigi a kan al'ummar Sudan da keta hurumin shugabancinsu.

373943


captcha