Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga ofishin shugaban kasar Iran cewa; a wata zantawa da ta hada shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinejad da wasu jami'an gwamnatocin kasashen Mali da Gambia da suka hada da shugabannin majalisun dokokin kasashensu, ya bayyana cewa nauyi ne da ya rataya kan al'ummar musulmi da su mara wa al'ummar palastinu baya, wajen tunkarar zalunci da danniyar Haramtacciyar Kasar Isra'ila, wanda kuma hakan shi ne babban abin da al'ummar Palastinu ke bukata daga musulmi kafin komai.
Shugaban na Iran ya kara da cewa; daya daga cikin muhimman abubuwan da Iran ta sa gaba kansu a halin yanzu shi ne, kara karfafa dangantaka da kasashen Afirka, domin a cewarsa kasashen Afirka suna da matsayi na musamman a wajen Iran, kuma da sannu za su cimma matsaya ta fuskacin musayar ilmomi, kuma a shirye take ta byar da ilimomi ga kasashen Afirka.
374019