IQNA

Kur'ani Ya Yi Bayani Kan Halittu Da Hanyoyin Rayuwarsu A Ilmance

Bangaren adabi: Shugaban jami'ar Zahra(AS) ya bayyana cewa; duk da cewa kur'ani mai tsarki ya zo ne sama da shekaru dubu daya da dari hudu da suka gabata, amma kuma ya kawo bayanai a ilmance dangane da halittu da yanayin rayuwarsu gami da kissoshi.
A wata zantawa da ta hada shugaban jami'ar Zahra (AS) (Mahbuba Mubashiri) da kamfanin dillancin labaran Ikna ya bayyana cewa; kur'ani mai tsarki littafi ne mai fadi ta fuskacin ma'ana, duk da cewa a bangaren fusahar magana kur'ani ya shahara wajen fifikonsa fiye da kowa da komai, amma kuma a bangare guda kur'ani ya kawo bayanai na ilimi kan halittu da salon rayuwarsu, wanda hakan ke tababtar da cewa shi littafi ne da ya kunshi komai dad an adam ke bukatar sani domin kamala. A bangare guda kuma malamin ya tabo batun kissoshi da ke cikin kur'ani mai tsarki, inda ya bayyana cewa kur'ani ya kawo kissoshi bisa tsari mai gamsarwa, misali kisser annabi Yusuf ta zo cikin kur'ani bisa wani tsari mai banshawa, tare dab urge mai karantawa ko mai sauraro, kamar yadda kuma ya kawo kissoshin a takaice amma kuma masu ma'ana.

374068