Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; za a gudanar da taron ne a birnin Tehran, wanda zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar, gami da dalibai 'yan kasashen waje da suke karatu a cibiyoyin ilimi na Iran.
Daya daga cikin masu shirya gudanar da taron (Mehdi Sheikhlu)
Ya bayyana cewa babbar manufar gudanar da wannan taro ita ce; karfafa matsayin hadin kai tsakanin al'ummar musulmi, kuma za a gudanar da taron a lokutan da ake gudanar da tarukan makon hadin kai, wanda mu'assisin jamhuriyar musulunci ta Iran ya assasa, da nufin ha kan al'ummar musulmi wuri guda, tare da ajiye banbance-banbance wuri guda, tare da haduwa kan babbar manufa ta tauhidi, da riko da sakon msulunci wanda shi ne babbar manufa.
374713