Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da taro a Gaza mai take (Qods cibiyar al'adun laraba) wanda ke tabbatar da cewa al'ummar larabawa da na musulmi na nan daram kan batun Qods.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (Ma'an) cewa; an fara gudanar da taro ne a daren jiya, inda dubban palastinawa mazauna yankunan zirin Gaza suke halarta, domin tabbatar wa duniya musamman yahudawan sahyuniya masu daure musu gindi a duniya da su kwana da sanin cewa; al'ummar Palestinu da sauran al'ummomin larababawa da na musulmi suna nan daram kan bakansu, dangane da batun Qods da matsayinta a wurinsu.
Shugaban kwamitin kula da al'du da batun Qods da hukumar Hamas ta kafa (Ata'ullah Abu Al-sabah) ya bayyana cewa; manufar gudanar da taron ita ce tabbatar wa duniya cewa al'ummar palastinu ba za su taba yin watsi da batun Qods da wajibcin 'yanto ta daga danniya yahudawan sahyuniya ba.
374708